HOME

TRICKS

BLOGGING

MOBILE
WELCOME TO TIPS24 BLOG ENJOY YOUR LIFE WITH NEW TRICKS FOR BOTH MOBILE AND PC, [If You Find Copyright Content Kindly Report It To 08168983354 Thank you]
entclass-bg

 
Yadda Ake Generating Na Privacy Policy Page Setup 2020
Assalamu alaikum barka da zuwa shafin tips24 wannan shafi ne da yake kawo muku Tricks gameda Blogging da kuma matsalolin wayoyinku da Computer

ABUBUWANDA KE CIKI:-


 • Sharhi gameda Policy page
 • Yadda ake generating na policy contents
 • Yadda ake saita Privacy Policy contents

SHARHI GAMEDA POLICY PAGE


A yau darasin namu zaiyi waiwaye ne gameda Privacy  Policy page wato wannan wata page ce wanda take da muhimmanci sosai saboda kuwa wannan page din a sabon policy na GOOGLE ADSENSE sun bada karfi sosai wurin binciken policy page na blogger saboda ana samun COPY COPY a page na mafi yewancin bloggers.
Ana samun Reject daga google adsense sakamakon wannan Covid19 din saboda kuwa abin ya shafi Advertisers nasu wannan yasa google adsense suka tsaurara dokokinsu ga publishers wanda dole kana bukatar cikasu kafin ka samu adsense approval.

YADDA AKE GENERATING NA POLICY CONTENTS

 Zamu fara generating na privacy policy contents kafin saita wa.Ga yadda ake generating na privacy policy:-
Da farko ka shiga wannan site din PRIVACYPOLICYGENERATOR

Bayan ya bude saiku cike form nan duk sunan BLOG naku zaku saka saidai na karshen ya zamana URL ne kamar yadda kuke gani.

Sai kayi Tick kamar yadda kake gani a wannan hoton na karshen ne NO kawai daga nan saika danna NEXT
Zabi country naka da state sannan ka saka gmail naka daga nan saika danna GENERATE MY POLICY
Saika COPY shi daga nan sai kaje privacy policy page na BLOG naka sai kayi paste nasa shikenan
DAFATAN WANNAN DARASI YA TAIMAKA SOSAI IN AKOI ABINDA BAKA GANEBA ZAKA IYA COMMENT DON MU TAIMAKA MAKA

Convert Airtime To Cash Cikin Sauki Automatic MachineAssalamu Alaikum Barkanku da War haka Kuma Barkan ku da Zuwa Shafin Tips24 Wannan shafin Mai Albarka Yana kawo muku Tricks Na Abinda Ya shafi Blogging Computer da Awayar Salula.

Automatic Airtime convert Machine


A yau Insha Allah Zan gabatar muku Da wani Website inda zaka convert na Airtime wato Katin waya Zuwa Cash,

Wannan Shafin Yana Aiki 100% bakada Matsala Zaka sayar da Airtime naka Wanda Aka Saka A waya Ko kuma Wanda Ka saya Wato Katin CREDIT,

Wannan Zai Taimaka sosai Saboda Ana Samun wasu Mutane Masu Mistake Wurin Recharge Ta Bank Wani Lokacin Mutum Nason Saka 100 saiya Saka 1000 da ma Kamantan su.
To share hawayenki wannan website din mallakar Wata sabuwar company ne mai Suna Victexstar.

Kar in cika ku da Surutu Abinda zakayi Shine Kashiga wannan Website din

Victexstar
Ka Tabbata kayi amfani da Browser Bayan ya bude Website din
Sai kayi Register daga nan Zai kaika Dashboard naka anan Zakaga Services nasu Saiku Shiga CONVERT AIRTIME TO CASH

System nasu automatic ne zai Gudanar da Aikin cikin Minti Biyar Kacal 5
Dafatan wannan Post din Ya Taima Keku Sosai.

Kuyi Comment Domin Kara mana Karfin guiwa.
How To Run Java Application On Android Device In HausaAssalamiu alaikum a yau insha Allah nazo mmuku da yadda ake Running na JAVA APP ko JAVA GAMES  a waya kirar cikin sauki.
Sanin kowa ne lallai java phone sun shigo Da fasaha kala kal hakan yasa suka shara a shekarun baya wanda Hakan Yasa Akayi musu Application masu kyau harda Games masu jan hankali.

Kada In cika mu da Surutu Bari muje kai tsaye Izawa ga Darasin namu akoi kafin gudanar da Wannan Aiki Lallai muna Bukatar Application na Android wanda zai Taimaka mana Wojen Aiwatarda Wannan Aiki.

Saboda haka ba tareda Bata Lokaci ba Ku shiga wannan Alamar ta Download Domin Saukarda Wannan Apk din.

DOWNLOAD JBED

Wannan Application din An Ginashi ne Domin Taimakawa Gurin bude java app a Wayar ta android Kamar dai yadda Kukasan Cewa ana Iya Bude Application na Android A Computer to haka ma Wannan Insha Allah zaka bude Java App da Games naka Dama Sauran programs din cikin sauki sannan Offline ne.

Na Tabbata wannan Application din zai taimaka Sosai Wojen Tunowa da wasu Java games da Apps irinsu 2go da dai sauran abinda sukayi fice musamman Lokacin Symbian.

Yadda Zaka Saita Edge Lighting A Wayarka Ta Android

                                 
                             

Assalamu alaikum a yau insha Allah zan nuna muku yadda zake saita EDGE LIGHT a wayar android kafin mu fara wannan darasin zanso kusan menene EDGE light wannan wani application ne wanda zai baka damar saka light style a gefen screen naka na wayar android sannan kuma wannan LIGHT din yana dauke da COLOURS masu yewan gaske wato a taikai ce wannan wutar zai zama ado ne ga wayarka sannan kuma yana aiki da NOTIFICATION na waya wato kamar dai blink light saidai shi wannan yana zagaye ne a gefen screen naka gaskiya wannan APK din yana da matukar abin burgewa sosai wannan yasa nakeson na koya muku yadda zaku saita shi yanzu ba tare da bata lokaci ba bari muje kai tsaye zuwaga darasin da farko ku bi wadannan matakan domin sauke wannan apk din please bazamu bada link ba saidai kuje play Store ku dauko sa saboda wasu dalilai na blog namu

zamu wannan darasin cikin screenshort da duma rubutu saboda haka zanso kuga yadda wannan application na EDGE LIGHTING yake saboda haka ku bi wadannan matakan kamar haka:-

Dafarko jeka PLAY STORE sai kayi search na (EDGE LIGHTING NOTIFICATION)
Bayan ya bude sa kayi dawnload nasa bayan ya gama download saika bude shi

 Wannan shine fuskar wayata kamar yadda kuke gani wannan style ne mai ban sha a wa sosai saboda kuwa zai zama abin burgewa wannan shine amfanin application din kawai

 Zaka iya zaban frame da kakeson ya zauna maka a lighting naka saboda ako frame da dama sannan zaka iya customizing na frame naka da kanka ta hanyar dannan wannan Alamar PLUS dake tsakiyar nan sai kayi generate na colors naka .


 zamu rika kawo muku sabbin android tips da tricks anan sabbi wadanda zasu taimakeku wurin gudanarda android phone naku sannan zaku iya ajiye mana matsalolin wayoyinku domin mu magance muku mun gode.

Yadda Ake Upgrade Na Network Daga 3G Zuwa 4GDon a ɗan wani lokaci, iskar da ke busa abubuwa akai-akai dangane da sadarwa a cikin ƙasa shine 3G da 4G. Da zarar mun ji Uku-G yana zuwa, baya sauraron sake, No-3G, Hudu-G yana zuwa. Mu, jama'a gaba daya, mun birkita da kalmomin iko. Mutane daga ko'ina cikin ƙasar suna jiran ɗan intanet mai sauri mai sauri. Kuma koda shekaru uku sun shude, ba za mu iya gyara shi ba - 3G, ko 4G! Don yin magana game da 3G, don yin tunani, cewa fasaha ta zamani kuma yanzu Duniya tana faɗaɗa hanyarta zuwa Hudu-G. Wanene za'a iya daukar nauyin alhakin wannan babbar asara a kasar?BTRC
Shin zaka iya gujewa wannan alhaki? Kafin mu shiga cikin wannan tattaunawar, bari mu sami wasu dabaru game da wannan fasaha ta 3G / Hudu-G.

Fasaha ta hannu guda uku-G da Hudu-kalmomi kalmomi biyu ne masu ban mamaki ga mutum daya. Amma suna iya tunanin abu ɗaya ne kawai bambanci tsakanin ukun da Hudu. To me yasa matsala sosai! Koyaya, talakawa ma suna buƙatar fahimtar kaɗan. Domin a halin yanzu kasuwar 3G tana cike da wayoyin salula na zamani 4G da 4G da Allunan. Idan baku da masaniya game da wadannan, to saidai sayen su na iya zama bata gari ne. Wani yana dawowa gida daga kasar waje. Tambaye shi ya kawo wayar zamani. Yana da babbar wayar salula hudu-G ta kawo muku. Don haka menene riba? Abu daya da za a iya tunawa, shine, cewa idan adadin ya kasance mafi girma, mafi kyawun sakamako zai zama.

YADDA ZAKA YI UPGRADE NA NETWORK NAKA DAGA 3G ZUWA 4G

Saika bi wadannan matakan don upgrade

STEP 1

bude phone's dialer naka saika danna wadannan  code *#*#4636#*#STEP 2

wannan zai daukeka zuwa  testing screen inda zaka samu options guda 4
 phone information, battery information, usage statistics, and Wi-Fi information.
STEP 3

Danna  ‘phone information.'

STEP 4


saika sauka kasa har sai kazo gurin ‘set preferred network type.'

STEP 5

a wurin preferred network type, zabi LTE/GSM/CDMA auto (PRL)STEP 6

saika sauka can kasa kuma zaka ga update button saika danna.

STEP 7

daga nan wayarka ta koma 4G daga nan indai area naku akoi 4g to zaka ga ya baiyana 

Yadda Zaka Saurari Wakoki Biyu A Lokaci Daya Kowani Kunne Da Wakarsa A EarphoneAssalamu alaikum zamu koyi yadda zaka saurari wakoki biyu a EARPHONE guda daya wato abinda nake nufi anan shine zaka iya playing audio guda biyu amma a ko wani kunne da nasa wakar  

misali zaka iya sakawa kunnen hagu(left) wakarsa daban sannan zaka iya sakawa kunnen Dama(right) wakarsa daban shima, kaga kenan zakayi listining na wakoki biyu a lokaci daya.
kamar yadda aka sani akoda yaushe TECHNOLOGY yana kara habaka ne saboda haka wannan ba abin mamaki bane musamman ga wadanda suke bibiyar INTERNET saboda kuwa a kowani rana saika samu abin ban mamaki  a wanna duniyar tamu abinda kake tunanin bazaiyu ba shine yake yuwa saboda kuwa masana a wannan harkar bawai kwana sukeyi ba kullum aiki sukeyi tukuru domin gabatarwa da al,umma sabon abu wanda zai  taimaka musu wajen sauwake harkokin yau da gobe,

wannan yasa a ka samu wani dan indiya wanda ya kirkiro wannan application din wanda ayau zan gabatar muku shi wato APK mai Suna (SPLITCLOUD DOUBLE MUSIC) Wannan shine APK dai zai baka damar sauraron waka biyu a lokaci guda

kar in cika mu da surutu bari muje kai  tsaye ga darasin namu Dafarko dai mai karatu kasan cewa wannan APPLICTION ne na masu wayar ANDROID kadai saboda haka sai masu Softouch kawai.

YADDA ZAKA SAITA WANNAN APPLICATION DIN GASHI KAMAR HAKA:-
1.Dafarko shiga nan

DOWNLOAD NOW

 domin download na wannan APK din bayan ka gama download zai nuna maka open kamar yadda kuke gani a wannan hoton saika danna OPEN bayan nan sai ka dan jirashi ya Bude2.Bayan nan zai bude maka kamar haka saika danna Allow daga nan zai kaika cikin application din inda zaka ga PLAY guda biyu.

                                                         
ku lura dakyau zaku ga PLAYER LEFT da kuma PLAYER RIGHT saboda haka saika dora wa kowanne wakar da kake so kaji zaka iya dai dai ta volume na ko wannen su.wannan shine in akoi inda baka ganeba yi amfani da comment Box domin yin tamabaya.
KAR KU MANATA GA LINK NA APPLICATION DIN ANAN


Mun gode da kasancewa da tips24 zaku iya ci gaba da bibiyar mu domin samun tips and free browsing 

Gabatarwa Gameda Python Programming Language(Introduction)

Wannan Shine Gabatarwa Gameda Python Language wato Introduction.

Dafarko Menene Python?

Python Programming Language Ne wanda Ya Shara Sosai A duniyar Programming,
 wanda Guido van Rossum ya kirkira, kuma aka sake shi a 1991.

Ana Aiki Da Python ta hanyoyi kamar haka:-


 1. web development (server-side).
 2. software development.
 3. mathematics.
 4. system scripting.


Menene Python Yake Yi?
 • Python yana Aiki Gurin webapplications. wato Gina Manhajar Websitd.
 • Python Yana Amfani gurin gina Da Kula Da Aikin Gudanarwar manhaja
 • (workflows).
 • Python yakan Gudanarda Rumbun bayanai Wato Data Base Ta hanyar gudanarda Hade-haden Bayanan.
 • Python yakan Iya Gudanar Da Sarrafa Bayanai Masu Yewa cikin kankanin lokaci Sannan Yana Iya Gudanar da Lissafi Cikin sauki.


Wadannan Kadan Daga Cikin Abinda Python Programming Language Yake aiwatar wa kenan Amma Suna Nan Da Dama Inku ka ci gaba Da bibiyar mu zamu rika Kawo Muku daya Bayan Daya

MEYASA AKE SON PYTHON?
Ga dalilanda yasa Ake Son Python programming Kamar Haka:-

Python Yana Aiki A Platform Ma babbanta Kamar su MAC, Windows, Raspberry Pi, Linux.

Python Yanada Syntax Mai Sauki kamar Na Turanci.

Python Yanada Syntax wanda yake Ba Programers Damar Rubuta Program Cikin Dan Karamin code ba tare Da Yewaita code ba.

Python Yana Aiki a INTERPRETER SYSTEM ta yadda idan Kayi Running Na Code nan Take Zai Aiwatar ba bata lokaci

Sannan python Yana Nan Version version ne
Saboda haka Yanada Kyau In zaka koyi python To ka fara daga mataki na farko
Wannan yana daga cikin abinda yake ba Hausawa Wuya sosai, ida. mutum zai koyi abu Maimakon ya fara daga Matakin farko saiya Tsallaka Yaje mataki na Biyu ko Na Uku Shiyasa Zaka ga Mutum Ya Fara Koyon Abu sannan Ya Watsar Dashi Daga Baya Saboda baima Fahimci menene Abun ba..

Yadda Zaku Sayi 300 Airtime Akan 60# A Ko Wani Layin AirtelAssalamu Alaikum Barka da zuwa tips24 Wannan shafin yana kawo muku Tips Da free browsing da cheap airtime and Data Cikin Harshen Hausa.
A yau Insha Allah Nazo Muku Da wata Hanya Da zaku Mori Airtel Call Sosai Wannan Hanyar Airtel Ce Ta Kirkireta Domin Sauwake Call Sun kirata Da CHEAP CALL.
Wannan Cheap Call Din Zai Baka Damar Samun Katin Naira 300# Akan 60# Kacal
Ga Yadda Airtel suke Tura Wannan Sakon

Enjoy 5 times airtime on your line. Pay N60 & get N300 to text & call ALL NETWORKS in Nigeria.

Gaskiya Wannnan Airtel. n Kudin yana Da Matukar Karfi ba irin sauram Bonus Masu Tafiya Da wurin nan Bane.
Sannan Wannan Tsarin Kusan Ko wani Irin Layi Yana Yi.

Kar in cika mu Da Surutu Bari muje kai tsaya Ta yadda zaka Samu Wannan Kudin Kiran Ba wani abu mai Wuya Bane Dafarko ka Tabbata Ba, a Binka Bashi

Sannan Saika Sayo Katin 100 Sai kayi Recharge ta Hanyar Dannan *126*
Wato Normal Recharge zakayi Bawai Irin na *555* Ba Saboda Yewancin mutane Yanzu Sun Koma Recharge Da 555 Saboda  Akoi Bonus.
Bayan Ka Saka Card Naka Saika Dannan

*234*60#


Saika Tura Zasu cire Naira 60 zasu baka 300
Wannan 300 Din zaka Iya Kiran Ko Wani Irin Layi A Nigeria nan Saboda Bata Selecting Network.
Wadannan Sune Kawai Hanyarda Zaku Samu 300 Airtime Akan 60 A Layinku Na Airtel.
Idan Akoi Inda Baka Gane Ba Kayi Tambaya Saboda A warware Maka Matsalarkan.  Mun gode da Ziyartar Tip24 Blog No 1 Hausa Tech Blog Muna Tare Daku Akoda Yaushe Insha Allsh.

Yadda Zaka Sayi Data 1.5gb Akan 500 Valid 14days


Wannan Bonanza ne ga Masu layin Glo.

Assalamu alaikum a yau insha Allah zamuyi bayanin yadda zaka samu Glo Mb wato yadda zaka samu 1.5GB akan naira 500 kacal sanin kowa ne kwanakin nan glo sai sabbin cheat suke fitowa dashi saboda haka nema ake ta samun bonanza musaman masu browsing don kusan zance masu browser sunfi kowa morewa layin glo musamman dub da yadda zance kamar ma layin glo ne a baya bayan nan wajen kira saboda reshin farin jinin shi amma a yanxu insha Allah kamfanin sun taso suna aiki tukuru saboda inganta tsarin nasu musamman masu browsing ne zasu fi morar su.
Wannan kuma ya taimaki  layin GLO sosai domin kuwa kwannnan nan Customers nasu sai karuwa sukeyi musamman idan glo din suka fitar da wani sabon tsarin sayan data saika kaga mutane na cincijidon sayan layin musamman idan sukace sai sabon layi yake yi a yanzu zance kusan BLOGGERS namu ba wanda bai mallaki layin glo sama da hudu 4 ba kuma duk ta dalilin wannan tricks da suke fitar wa ne.
kuma masu hada VPN suna ba kamfanin na glo wahala sosai saboda kuwa mafi yewancin Vpn da ake hadawa anfi hada free browsing na camfanin ita Glo duba da yadda basu daukan mataki kwakkwara Hakan kuma ya faru ne sakamakon reshin kwararrun mai aikata da kamfanin ke fama dashi wannan shine.
Wato wannan MB din Yayi sauki sosai duba da yadda Alummar Mu ke fama Da sayan MB,
Wannan MB din Normal Mb ne wato yana Iya aiki A ko wanne irin platform irin Facebook Twitter Whatsapp Instagram Wechart Eskimi Google Website da Duk wani Platform zaka iya Shiga Da wannan Data Din Sannan Kuma Wannan MB din yana Aiki A ko wace irin Naura/Device
Ma, ana ba, a Taskance cewa Sai Android Ko Windows ba A, A zaka iya Browsing dashi A laptop Da wayar ka Ta Salula.
Kar In chika Mu da Surutu Bari muje ga yadda Ake sayan Wannan DATA din.

YADDA AKE SAYAN DATA 1.5 AT 500 A LAYIN GLO

Shidai wannan Data din ya Kasu gida Biyu Akoi na 1.5GB akan 500 Yana Kwana 14
Sannan Akoi na 200MB yana aiki 12AM to 5AM). Na safe
Zaka Ga hakan inka danna *777#
Domin sayan wannan DATA danna *777# kayi reply da 1 ka sake reply da 1  


Ka tabbatar ka sake Reply Da lamba 1 Saboda ka samu auto Renew
Wannan Data Yana Kwana 14 Kamar yadda na Gaya Muku. 
Domin duba wannan Data din zaku iya danna Wadannan Lambobin kamar haka
*127*0#.

Kamar yadda Kuka Gani a wannan Hoto Akoi wasu Data Plans A gurin Wanda Zaku Iya Sayan Sun in kuna So amma Dai na 1.5gb inaga Yafi Sauki Da yewa

Idan Akoi Inda Baka Gane Ba Xaka Iya Mana Tambaya
Ta Hanyar amfani da Comment box 
Daga Freeblog Team